Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Cibiyar musayar kayayyakin Ghana za ta farfado da ci gaban jin dadin rayuwa da tattalin arzikin Afirka
2019-09-03 09:48:50        cri

Ministan abinci da aikin gona na kasar Ghana, Owusu Afriyie Akoto, ya bayyana cewa, cibiyar musayar kayayyaki da aka kafa a kasar, za ta mayar da hankali wajen farfado da ci gaban jin dadin jama'a da tattalin arzikin kasar da ragowar kasashen dake nahiyar.

Da yake karin haske yayin wata zantawa da kamfanin dillacin labarai na Xinhua, ministan ya ce, cibiyar, wadda ita ce ta farko a Afirka, za ta rika sayar da hatsi, gahawa da koko a cikin kasashen nahiyar da kasuwannin ketare, a wani mataki na kara samun damar yin takara.

Ya ce, cibiyar za ta janyo hankulan ragowar ministoci daga kasashen Afirka, su zo su yi kasuwanci. Don haka ya bukaci kasashen Najeriya, da Cote d'Ivoire da sauran kasashen nahiyar, da su shigo a dama da su, don cin gajiyar wannan cibiya.

Akoto, ya kuma yiwa Xinhua bayani game da wannan batu, yayin sabon dandalin shugabanci na Afirka da ya gudana a Accra, babban birnin kasar. Ya ce, kasarsa, tana son zama cibiyar kasuwanci a Afirka, inda za ta jagoranci harkokin cinikayya a nahiyar, tare da zakulo damammaki na fasahar zamani don kara yawan amfanin da ake shukawa, ta yadda za a samar da isasshen abinci.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China