Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Guterres ya yi kira a kara maida hankali kan unguwanni yayin raya birane
2020-11-01 16:45:52        cri

Jiya Asabar 31 ga watan Oktoba, rana ce ta bikin ranar birane ta duniya, babban sakataren MDD Antonio Guterres ya gabatar da wani rahoton murnar ranar ta kafar bidiyo, inda ya bayyana cewa, a ranar birane ta duniya ta bana, ya dace a kara maida hankali kan rawar da unguwanni suke takawa yayin da ake raya biranen kasashen duniya.

Babban jami'in ya yi nuni da cewa, a halin yanzu, al'ummun kasashen duniya kaso 55 bisa dari suna rayuwa ne a cikin birane, kuma bisa hasashen da aka yi, adadin zai iya karuwa zuwa kaso 68 bisa dari nan da shekarar 2050, musamman yayin da ake kokarin dakile annobar cutar COVID-19, rawar da unguwannin birane suke takawa tana kara janyo hankalin mutane.

Ya kara da cewa, yaduwar cutar COVID-19 ta jefa tsarin kiwon lafiyar kasa da kasa cikin mawuyacin hali, a karkashin irin wannan yanayi, unguwannin biranen kasashen duniya suna takawa babbar rawa domin kiyaye tsaron al'ummun kasa da kasa, ta hanyar gudanar da hadin gwiwa dake tsakaninsu da gwamnatoci da kuma nuna goyon baya ga matakan kandagarkin cutar da gwamnatocin suka dauka.

Guterres ya jaddada cewa, idan unguwannin birane suka shiga aikin tsara manufofin gwamanti ko kuma suka samu kasafin kudin gwamanti, to za su taimakawa ci gaban birane mai dorewa.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China