Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwamitin sulhun MDD ya sabunta wa'adin aikin wanzar da zaman lafiya a yammacin Sahara na shekara guda
2020-11-01 16:29:42        cri

A ranar 30 ga watan Oktoba, kwamitin sulhun MDD ya sabunta wa'adin aikin tawagar wanzar da zaman lafiya a yammacin hamadar Sahara wato MINURSO da karin watannin 12.

Kudirin dokar mai lamba 2548, ya ambato mambobin kwamitin sulhun MDD 15 sun tsawaita wa'adin aikin tawagar ta MINURSO har zuwa ranar 31 ga watan Oktoban shekarar 2021.

Kudirin ya jaddada bukatar neman cimma hakikanin burin da ake da shi da hasashen da aka yi na warware matsalolin siyasar kasashen shiyyar yammacin hamadar Sahara bisa ga tsarin yarjejeniya da muhimmiyar hadin gwiwar da tawagar MINURSO za ta yi bisa taimakon MDD don cimma wannan buri.

Majalisar ta bukaci dukkan bangarori da su koma teburin sulhu da kyakkyawar manufa karkashin jagorancin babban sakataren MDD kuma ba tare da gindaya wasu sharruda ba, kuma a dora kan kokarin da aka faro tun daga shekarar 2006, da kuma lura da irin nasarorin da aka cimma a halin yanzu don samun nasarar kaiwa ga matakin karshe na warware rikicin siyasar wanda kowane bangare zai iya gamsuwa da shi, wanda zai gamsar da al'ummar kasashen shiyyar yammacin hamadar Sahara karkashin manufofi da yarjejeniyar MDD, kana an kuma jaddada muhimmancin rawar da kowane bangare zai taka kan wannan batu.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China