2020-10-25 16:27:13 cri |
A jiya Asabar zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya gabatar da wani rahoto ta kafar bidiyo yayin da ake murnar ranar MDD, inda ya ya yi kira da a goyi bayan ra'ayin cudanyar bangarori daban daban da aikin MDD da kuma kara karfafa hada kai da hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa.
Zhang Jun ya kara da cewa, ranar MDD ta bana tana da ma'ana ta musamman, saboda ana fama da manyan sauye-sauyen da ba a taba ganin irinsu ba a cikin shekaru dari daya da suka gabata, kuma ana fama da rikicin da annobar COVID-19 ke haifarwa, kana ana fama da babban kalubalen nuna bangaranci da ba da kariya da zalunci, a don haka, al'ummun kasashen duniya suna yin la'akari cewa, wace irin MDD ce ake bukata? Ta yaya za a gina kyakkyawar makomar bil Adama?
Hakika, yayin taron shugabannin kasashen da aka shirya domin taya murnar cika shekaru 75 da kafa MDD, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da dabarun kasar Sin, inda ya bayyana cewa, akwai tsari daya kacal a duniya wato tsarin duniya dake karkashin jagorancin MDD, kuma akwai ka'ida daya tilo a duniya wato ka'idar huldar kasa da kasa da aka tsara bisa ka'idar MDD, yanzu haka ya dace MDD ta kara maida hankali kan aikin tabbatar da adalci domin ingiza hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa.
Kana ya yi nuni da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da nacewa kan manufar cudanyar bangarori daban daban, kuma za ta ci gaba da goyon bayan ka'idar MDD da dokokin kasa da kasa, tare kuma da goyon bayan ayyukan MDDr.
A ranar 24 ga watan Oktoban shekarar 1945, ka'idar MDD ta fara aiki a hukumance, lamarin da ya alamta cewa, an kafa MDD a hukumance, a shekarar 1947, an zartas da kuduri a babban taron MDD, inda aka tsaida kuduri cewa, za a kebe ranar 24 ga watan Oktoba a ko wace shekara domin ta kasance ranar MDD.(Jamila)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China