Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD: Bangarorin Libya sun cimma matsaya kan muhimman batutuwa
2020-10-22 13:51:13        cri

Bayan shafe tsawon kwanaki biyu ana gudanar da tattaunawar gaba da gaba ta kai tsaye a tsakanin wakilan bangarori biyu na kasar Libya karkashin hukumar hadin gwiwar sojoji ta 5+5, a halin yanzu, bangarorin biyu sun cimma matsaya kan wasu muhimman batutuwa masu yawa wadanda za su yi matukar tasirin kai tsaya ga zaman rayuwa da walwalar al'ummar kasar Libyan, wakilin MDD ne ya bayyana hakan a ranar Laraba.

Stephanie Williams, mai rikon mukamin wakilin musamman na babban sakataren MDD, kana shugaban tawagar jami'an wanzar da zaman lafiyar MDD dake Libya UNSMIL, ya bayyanawa taron manema labarai cewa, bangarorin biyu za su ci gaba da tattaunawa kan batutuwan da za su kai ga samun nasarar cimma matsayar kulla yarjejeniyar tsakaita bude wuta.

A cewar Williams, wakilan bangarori biyu na Libya, sun amince za su bude hanyoyin dake hada dukkan shiyyoyi da biranen kasar Libya, wanda hakan zai yi matukar tasiri da kawo ci gaba ga zaman rayuwar al'ummar kasar Libya.

Sannan sun kuma amince za su bude hanyoyin sararin samaniyar kasar Libyan, musamman harkokin sufurin jiragen sama zuwa Sebha, wanda shi ne babban birnin mulki na shiyyar kudancin Libya.

Wakilan sun kuma amince za su daina amfani da kalaman nuna kiyayya, za su goyi bayan tsarin yanayin da ake ciki a yanzu na tabbatar da kwanciyar hankali da kuma daina amfani da matakan soji, kana za su goyi bayan yunkurin yin musayar fursunoni a tsakaninsu.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China