Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Africa CDC: Ya kamata kasashen Afirka su shirya fuskantar zagaye na 2 na bazuwar COVID-19
2020-10-30 11:33:10        cri
Babban daraktan hukumar kandagarki da shawo kan cututtuka masu yaduwa a Afirka ko Africa CDC Mr. John Nkengasong, ya yi kira ga kasashen nahiyar da su shirya fuskantar yiwuwar bullar cutar a zagaye na biyu.

Mr. Nkengasong ya yi wannan kira ne a jiya Alhamis, lokacin da yake jawabi ta kafar bidiyo, ga wani taro na masu ruwa da tsakai, inda ya ce ya zama wajibi nahiyar Afirka ta yi shirin tunkarar sake bazuwar wannan annoba a zagaye na biyu, musamman ganin yadda yawan masu harbuwa da ita a baya bayan nan ya dan karu.

Babban jami'in ya kuma bukaci kasashen na Afirka, da su karfafa shirin su na sanya ido, su kara fadada yin gwaji, tare da sanya sassan al'ummun su cikin aiwatar da matakan kandagarki, kamar sanya marufin baki da hanci, don tabbatar da cimma nasarar yaki da cutar yadda ya kamata.

Nkengasong ya ce "Idan mun yi aiki cikin hadin gwiwa, za mu iya tunkarar zagaye na 2 na wannan cuta, wanda tabbas yana nan tafe. Ina nufin muna iya ganin hakan a kasashen turai. Muna son tabbatar da mun kare nasarorin da muka samu, cikin sama da watanni 10 da suka gabata".

Ya zuwa jiya Alhamis, Africa CDC, kwararriyar hukumar lafiya karkashin kungiyar AU, ta tabbatar da harbuwar mutane 1,748, 335 da cutar ta COVID-19 a sassan Afirka, ciki hadda mutum 42,151 da cutar ta hallaka. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China