Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Afrika ta kudu: Bunkasa kayayyakin more rayuwa zai taimakawa tattalin arzikin kasar
2020-10-28 10:49:08        cri

Shugaban kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa ya ce, bunkasa ayyukan more rayuwa zai taka muhimmiyar rawa wajen farfadowar tattalin arzikin kasar Afrika ta kudu wanda ya tsaya cik, shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin bikin bude otel da kuma cibiyar taruka da aka gina a gabashin birnin Johannesburg.

Ya ce gwamnatin kasar tana kokarin mayar da hankali wajen sabbin ayyukan ababen more rayuwa, matakin dake da muhimmanci wajen samar da guraben ayyukan yi.

Shugaban ya ce yayin da annobar COVID-19 ta yi wa tattalin arzikin illa, yana da kwarin gwiwar zai farfado.

Ya ce yana da muhimmanci a farfado da guraben ayyukan da aka rasa a sanadiyyar barkewar annobar kuma a samar da wasu ayyukan sabbi, ya kara da cewa, matukar dai kasar tana son janyo jarin kasashen waje, to ya zama tilas masu zuba jari na cikin gida su zama a sahun gaba.

Tun da farko Ramaphosa ya bayyana cewa mutum-mutumin OR Tambo mai tsawon mita 9 da aka gina a lambun shakatawa dake Kempton, yana daga cikin muhimman abubuwan dake janyo hankalin masu yawon shakatawa zuwa kasar. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China