Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD: Mutane miliyan 5.2 zasu bukaci agaji a Somali a shekara mai zuwa
2020-10-29 11:21:03        cri
Hukumar samar da jin kai ta MDD ta ce, kimanin mutane miliyan 5.2 ne za su bukaci agaji a shekarar 2021 a kasar Somalia a sanadiyyar matsalolin sauyin yanayi, kama daga matsalar ambaliyar ruwa, farin dango, da kuma hare haren kungiyoyin 'yan bindiga da ke tabarbarewa ga kuma annobar COVID-19 da ake fama da ita.

Ofishin kula da shirin samar da jin kai na MDDr OCHA, ya sanar cewa, matsalolin ayyukan jin kai a Somalia sun kasance mafi sarkakiya, kuma mafi hadari a duk duniya. Kimanin mutanen kasar miliyan 2.6 ne ke rayuwar a sansanoni bayan sun kauracewa muhallansu, sannan an sake samun sama da mutanen Somaliya miliyan 1 da suka kauracewa muhallansu a cikin wannan shekarar.

Muddin basu samu tallafi ba, ana sa ran matsalar karancin abinci zata iya samun karuwa mutane miliyan 1.3 zuwa mutane miliyan 2.1 da zasu bukaci taimako ya zuwa watan Disamba.

Sai dai kuma, duk da kalubalolin, hukumar OCHA ta sanar cewa, MDD da masu samar da taimako sun bayar da taimako ga mutane sama da miliyan 2.3 a wannan shekarar.

Amma masu bayar da agajin sun ce kudaden da ake bukata a kowane bangare bai wadatar ba, yayin da sama da kashi 50 na bangarorin sun samu kasa da kashi 35 ne na adadin kudaden da suke bukata.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China