![]() |
|
2020-09-18 10:30:56 cri |
Shugaban kasar Somaliya Mohamed Farmajo, da shugabannin shiyyoyin kasar 5 a ranar Alhamis sun kammala wani taron kwanakin biyar a Mogadishu, inda suka amince da yin sauye sauyen a tsarin salon zaben kasar na shekarar 2020/21 wanda ke da matukar muhimmanci ga zaman lafiyar kasar.
Farmajo, wanda ya karbi bakuncin shugabannin shiyyoyin jahohin Galmudug, da jahar kudu maso yammaci, da Hirshabelle, da Puntland da kuma Jubaland, da magajin garin Mogadishu, sun amince da gudanar da sauye sauye masu yawa kan yarjejeniyoyi uku na lokutan baya game da zaben kasar, inda suka cimma matsaya a taron na Dhusamareb, babban birbnin jahar Galmudug.
A sanarwar hadin gwiwa wanda ofishin shugaban kasar Farmajo ya fitar ta ce, gwamnatocin kasar da na shiyyoyin kasar za su nada hukumomin zabe domin tafiyar da al'amurran zaben kasar yadda ya kamata.(Ahmad)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China