Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan FDI na duniya na farkon rabin bana ya ragu da kimanin kashi 50 cikin dari
2020-10-28 13:32:50        cri
Bisa rahoton da kungiyar taron ciniki da bunkasuwa ta MDD ta gabatar a jiya, an ce yawan jarin da kasa da kasa suka zuba kai tsaye a duniya wato FDI, a farkon rabin shekarar nan ta bana, ya ragu da kashi 49 cikin dari bisa na makamancin lokaci a bara, amma duk da haka ana kiyaye yawan FDI din a kasar Sin.

Shugaban sashen kula da zuba jari da harkokin kamfanoni na kungiyar Zhan Xiaoning, ya yi nuni da cewa, dalilin da ya sa aka kiyaye zuba jarin waje a kasar Sin shi ne, Sin ta kasance daya daga cikin kasashen da suka hana yaduwar cutar COVID-19, da mayar da samar da kayayyaki cikin hanzari, kana gwamnatin kasar Sin ta dauki matakan zuba jari masu amfani da sauki, don taimakawa wajen mayar da aikin zuba sabon jari na kamfanonin kasashen da waje suka sanar.

Zhan Xiaoning ya jaddada cewa, a sakamakon ci gaba da yaduwar cutar COVID-19 a duniya, wasu yankuna suna fuskantar hadarin tsanantar yanayin tinkarar cutar, don haka tsarin samar da kayayyaki da kamfanonin kasa da kasa suka kafa ya kara dogaro kan kasar Sin, kana wasu kamfanonin kasashen waje da suka zuba jari a kasar Sin, sun kara zuba jari ga Sin ta amfani da ribar da suka samu. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China