Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bankin Duniya: tattalin arzikin kasar Sin zai habaka da kaso 2 cikin dari a 2020
2020-09-29 14:36:11        cri
Bankin Duniya ya ce, ana sa ran tattalin arzikin kasar Sin zai karu da kaso 2 cikin dari a bana, adadin da ya karu da kaso 1 kan hasashen da aka fitar a watan Yuni.

Bankin ya bayyana cikin hasashensa na tattalin arzikin yankin Asia da Fasifik na Oktoban bana cewa, za a samu karuwar adadin ne bisa kashe kashen kudi daga gwamnati da fitar da kayayyaki zuwa ketare da kuma raguwar yaduwar cutar COVID-19 da aka samu tun cikin watan Maris, sai dai kuma, ya ce za a samu raguwar sayen kayayyaki a cikin gida. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China