Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An fidda rahoton dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya
2020-10-22 16:25:29        cri
Jiya Laraba, taron dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya ya fidda wani rahoto mai taken guraben aikin yi a nan gaba, inda ya bayyana cewa, dakushewar tattalin arziki sakamakon barkewar cutar numfashi ta COVID-19 da bunkasuwar na'urori masu kwakwalwa dake iya yin ayyuka da kansu, za su haifar da saurin sauye-sauye a kasuwannin samar da guraben aikin yi fiye da yadda aka tsinkaya.

Rahoton na nuna cewa, ya zuwa shekarar 2025, tsarin mai da na'ura ta yi aiki da kanta da tsarin raba ayyuka tsakanin mutane da na'urori za su kawo sauye-sauye ga guraben aiki miliyan 85 a fannoni 15. Sai dai an ce, za a samar da sabbin guraben ayyukan yi miliyan 97 cikin shekaru 5 masu zuwa, sakamakon sauye-sauyen tattalin arziki da yanayin kasuwannin samar da guraben aikin yi, wadanda za su shafi fannonin fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam, da kirkire-kirkire da sauransu. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China