Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan hatsin da Sin ke nomawa ya karu cikin shekaru biyar da suka gabata
2020-10-28 11:14:46        cri

Alkaluman baya bayan nan da ma'aikatar aikin gona da raya karkara ta kasar Sin ta fitar, sun nuna cewa, adadin hatsi da kasar Sin ke samarwa ga duk dan kasa karkashin tsarin samar da ci gaba na shekaru 5 kaso na 13, wato tsakanin shekarar 2016 zuwa 2020 zai ci gaba da haura kilogiram 470, yayin da adadin da kasashen duniya suka amince da shi bai wuce kilogiram 400 ba.

Wadannan alkaluma dai na nuna cewa, kasar Sin na samar da wadataccen hatsi ga jama'ar ta su biliyan 1.4. Kaza lika cikin shekaru 5 da suka gabata, yayin da al'ummar kasar ke kara samun ingancin rayuwa, jama'a na kuma sauya cimakar su daga neman koshi kadai, zuwa cin abinci sosai, kuma mai gina jiki.

Alkaluman sun kuma shaida cewa, fannin noma na kasar Sin na samar da karin yabanya mai inganci, mai kunshe da sama da nau'o'in abinci 49,200, wadanda ba sa kunshe da sinadarai, kuma ake samar da su daga yankunan kasar daban daban. Bugu da kari, wadannan nau'o'i na cimaka na isa zuwa ga kantuna da kasuwanni, domin amfanin al'umma cikin sauki.

A nan gaba kuma, Sin za ta ci gaba da maida hankali wajen tabbatar da daidaito a fannin noma amfanin gona, da kara yawan yabanyar dake shiga kasuwanni, tare da kara inganci, da kyautata damar yabanyar a fannnin shiga takara, a kasuwannin cinikayyar amfanin gona. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China