Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwararru sun bukaci a fara amfanin injunan noma a yankin kudu da Sahara
2020-09-29 10:38:44        cri

A ranar Litinin kwararru sun bukaci a samar da tsarin amfanin injunan noma na zamani domin taimakawa fannin ayyukan gona a yankin kudu da hamadar Saharar Afrika.

Kwararrun, sun bayyana hakan ne a wani taro ta kafar intanet a Nairobi, sun yi tsokaci cewa, amfani da injunan noma na zamani zai kawo gagarumin sauyi a sha'anin ayyukna noma a shiyyar.

George Marechera, manajan raya kasuwanci na gidauniyar bunkasa fasahar aikin gona ta Afrika dake Nairobi ya ce, rungumar yin amfani da manyan injunan noma na zamani zai samar da damammaki ga kananan manoma inda zai sauya tsarinsu daga noma don biyan bukatun iyali zuwa tsarin noman kasuwanci.

Marechera ya ce, amfani da manyan injunan noma yana kara samar da amfanin gona mai yawan gaske, da rage kudaden ayyukan kwadago, da samar da yabawa mai yawa a farashin mai rahusa kuma zai kara bunkasa tsarin cinikayyar kayan amfanin gonar.

Ya kara da cewa, akwai bukatar kasashen dake shiyyar su kaddamar da tsarin fara amfani da manyan injunan noma domin more fasahohin zamani da bunkasa ayyukan kananan manoma.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China