Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Guterres ya yi kira ga kasashen G20 da su kara azama wajen shawo kan cutar COVID-19
2020-09-04 13:02:01        cri
Babban magatardar MDD Antonio Guterres, ya yi kira ga kasashe mambobin kungiyar G20, da su kara azama wajen aiwatar da matakan shawo kan cutar COVID-19, da kuma gina tsarin farfadowa mai inganci.

Mr. Guterres ya gabatar da muhimman batutuwan tattaunawa 5, yana fatan kasashen na G20 za su amince da matsaya guda, game da matakan dage haramcin tafiye tafiye bisa shaidu na kimiyya.

Jami'in ya yi kira da a nazarci batun zuba jari a fannonin tsare tsare da ayyuka na zahiri, wadanda za su taimakawa shirin dawo da zirga zirgar matafiya cikin tsaron lafiya, da hadin kan sassa masu zaman kan su.

Guterres ya kuma yi kira da a dubi batun tsara manufofin kandagarkin yaduwar cutar, ciki hadda batun amfani da kayan gwaje gwaje, da bin diddigin masu dauke da cutar, da sauran matakai masu fa'ida na dakatar da bazuwar ta, da fadada bude hanyoyin zirga zirga masu karko.

Babban magatardar MDDr ya kara da cewa, abu ne mai muhimmnaci, martaba dokokin kasa da kasa na kare hakkin bil Adama, da 'yan gudun hijira. A kuma amince daukacin al'ummun duniya su ci gajiyar alluran rigakafi da ake samarwa a halin yanzu. Kaza lika su zamo masu arha, a kuma taimakawa ayyukan kiwon lafiya na duniya, da fannin sufuri na kasa da kasa, da kuma matakan farfado da tattalin arziki.

Ya ce "Kamata ya yi dukkanin ayyukan da za a gudanar, a yi su bisa martaba kimar dan Adam, da ka'idojin cudanyar kasashe daban daban." (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China