Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Irin shinkafa ya nuna amincin dake tsakanin Sin da Afirka
2020-09-18 18:51:06        cri

Duk da cewa, annobar cutar numfashi ta COVID-19 tana ci gaba da yaduwa a sauran sassan duniya, kana an yi fama da bala'in ambaliyar ruwa a wasu sassan kasar Sin, amma an girbe abinci a yanayin zafi a lardin Hunan a bana.

An shirya bikin mika abincin da gwamnatin kasar Sin ta samarwa kasar Sudan ta Kudu a Juba, fadar mulkin kasar a jiya Alhamis, inda ministan kula da harkokin jin kai da shawo kan bala'i na kasar Peter Mayen Majongdit ya nuna godiya matuka ga gwamnatin kasar Sin a madadin gwamnati da jama'ar Sudan ta Kudu.

Daga shekarar 1996 zuwa yanzu, ban da samar da tallafin abinci ga wasu kasashen Afirka, gwamnatin kasar Sin ta kuma tura masana aikin gona zuwa kasashen Mauritaniya da Ghana da Mali da Najeriya da sauransu a matakai daban daban, ta hanyar gudanar da aikin hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa, inda kwararrun suka yi kokarin yada fasahar noman shinkafa. Irin shinkafa ya nuna amincin dake tsakanin al'ummun kasar Sin da kasashen Afirka da yawansu ya kai sama da biliyan 2.

Yuan Longping kwararre a fannin fasahar noman shinkafa

Har kullum dattijo Yuan Longping wanda ya kware matuka wajen noman shinkafa yana mai da hankali kan yadda ake yada fasahar noman shinkafa a nahiyar Afirka da yadda ake taimakawa al'ummun kasashen Afirka samun isasshen abinci, a cikin 'yan shekarun da suka gabata, masana aikin gonan kasar Sin da yawan gaske sun je kasashen Afirka a matakai daban daban domin noman shinkafa a gonakin nahiyar.

Kana kamfanonin kasar Sin su ma sun kafa sansanonin gwajin noman shinkafa a wasu kasashen Afirka, haka kuma an yi nasarar shirya bikin baje kolin tattalin arziki da cinikayya na kasar Sin da kasashen Afirka karo na farko a lardin Hunan na kasar Sin tsakanin ranar 27 zuwa ranar 29 ga watan Yunin shekarar 2019, bikin da ya ingiza hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu wato Sin da Afirka.

A kwanakin baya bayan nan, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya je lardin Hunan domin kara fahimtar yanayin da lardin ke ciki a bangaren yaki da talauci, abun farin ciki shi ne, a cikin 'yan shekarun da suka gabata, lardin Hunan ya dukufa kan ci gaban aikin gona na zamani ta hanyar yin amfani da kimiyya da fasaha, inda ya taka babbar rawa wajen tabbatar da tsaron abinci a wasu kasashen duniya, ciki har da kasashen Afirka.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China