Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masana'antar Burodin Nang Tana Samar Da Wadata A Jihar Xinjiang
2020-10-26 15:54:18        cri

Duk wanda ya kai ziyara jihar Xinjiang, tabbas zai ci burodin Nang, wani irin abincin musamman na jihar.

A gundumar Payzawat ta jihar Xinjiang, an dukufa wajen kafa yankin masana'antar burodin Nang, inda aka nuna al'adu irin na wannan abinci, da samar da burodin Nang, yayin da kuma ake sayar da burodin Nang. An raya yankin bisa shirin inganta masana'antar Nang, da ba da horaswa, da samar da guraben aikin yi, da bunkasa harkokin yawon shakatawa, domin karfafa sana'o'in dake shafar burodin Nang, ta yadda za a samar da wadata ga al'ummomin yankin.

Ma'aikatan masana'antar za su sami horaswa ba tare da biyan kudi ba, bisa goyon bayan gwamnatin kasa, kana, bayan sun fara aiki a masana'antar, za a ba su daki da abinci. Mai kula da yankin masana'antar Ma Jun ya bayyana cewa, cikin ma'aikata guda 1200 na yankin, akwai mutane 696 da suka fito daga gidaje masu fama da talauci, amma a halin yanzu, dukkansu sun fita daga kangin talauci, suna iya samun kudin shiga har yuan 3500 cikin ko wace wata.

Abin farin ciki shi ne, ma'aikatan yankin suna yin aiki sa'o'i 6 zuwa 7 cikin ko wace rana, lamarin da ya sa, suke da lokacin kula da gonakin gidajensu.

Haka kuma, an kafa dakunan ziyara da nune-nunen al'adun burodin Nang a wannan yanki, ta yadda ba kawai masu yawon shakatawa za su iya kara saninsu game da al'adun burodin Nang ba, har ma za su iya yin irin wannan abinci da kansu.

Ban da haka kuma, yankin ya yi hadin gwiwa da jami'ar harkokin gona ta jihar Xinjiang, domin yin nazari kan yadda za a kiyaye Nang cikin dogon zangon sufuri, ta yadda, za a sayar da irin wannan abinci zuwa sassan kasar. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China