Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bunkasuwar Harkokin Yawon Shakatawa Ya Samar Da Wadata A Kauyukan Lardin Fujian
2020-10-23 15:49:17        cri

An fara aikin ginin tabo a lardin Fujian ne a karni na 11, kuma galibin gine-ginen tabon suna gundumar Nanjing, da gundumar Hua'an na birnin Zhangzhou da yankin Yongding dake birnin Longyan.

Ginin tabo na Changrong da Song Guihong da iyalinta suke zama yana kauyen Kanxia na garin Meilin na gundumar Nanjing dake birnin Zhangzhou, wannan gini yana da tarihi na sama da shekaru 100. A shekarar 2008 kuma, an shigar da ginin cikin jerin kayayyakin tarihi na kasa da kasa.

A shekarar 2011, an mai da yankin yawon shakatawa na gine-ginen tabo dake gundumar Nanjing a matsayin yankin yawon shakatawa na 5A, lamarin da ya sa, wadannan gine-ginen tabo suka taimakawa mazauna wurin wajen kawar da talauci da samun wadata. A shekarar 2015, Song Guihong ta dawo gundumar Nanjing domin yin aikin mai yin bayani a yankin yawon shakatawa.

Song Guihong ta ce, ita da mai gidanta ba su samu kudin shiga da yawa ba a lokacin da suka yi aikin kasuwanci a waje, amma, yanzu, ko wace shekara, tana iya samun kudin shiga yuan dubu 40 ta hanyar yin aikin mai yin bayani a yankin yawon shakatawa. A nan kuma, akwai sauki gare ta wajen kula da tsofaffi da yaransu.

A sakamakon gine-ginen tabo masu kyan-gani, yanzu akwai mutane masu yawa da suke zuwa wajen domin yawon shakatawa. Shi ya sa, matasan gundumar da dama sun dawo garuruwansu domin raya wannan aiki na yawon shakatawa.

Bisa labarin da aka samar, a shekarar 2019, gaba daya akwai mutane fiye da miliyan 6 da suka je yawon shakatawa a gundumar Nanjing, kuma kudin shigar da aka samu a fannin yawon shakatawar ya kai yuan biliyan 5.38. Ya zuwa yanzu, sana'ar yawon shakatawan ta samar da guraben aikin yi sama da dubu 80 ga mutanen gundumar Nanjing, inda aka bude otel otel kimanin guda 508 a wurin. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China