Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kafofin yada labaru na Iran sun ce, Iran za ta sanar da matakan mayar da martani kan Amurka
2019-05-07 14:05:45        cri

Jiya Litinin kafofin yada labaru na kasar Iran sun labarta cewa, gwamnatin kasar za ta sanar da wasu matakan mayar da martani kan kasar Amurka nan ba da dadewa ba, wadda ta janye jikinta daga yarjejeniyar batun nukiliyar Iran, da kuma maido da takunkumi kan Iran.

Kamfanin dillancin labaru na FNA na Iran ya ruwaito cewa, Iran za ta dauki wadannan matakai ne domin mayar da martani kan Amurka, wadda take sanya wa Iran takunkumi ta fuskar sayar da man futer a ketare da kuma tsarin bankuna.

Jaridar Tehran Times ta ce, gwamnatin Iran ta riga ta tsai da kuduri a hukumance na mayar da martani kan Amurka, wadda ta janye jiki daga yarjejeniyar batun nukiliyar Iran, tare da maido da takunkumi kan Iran. Kila Iran za ta soke kayyadewa kan wasu ayyukan nukiliyar Iran karkashin yarjejeniyar batun nukiliyar kasar. Har ila yau kuma, jaridar ta ruwaito wata majiya da ke da masaniya, amma ba ya so a ambaci sunanta na cewa, ko da yake Iran za ta dauki wadannan matakai, amma lamarin ba ya nufin cewa, za ta janye jiki daga yarjejeniyar batun nukiliyar ta. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China