2020-09-21 12:06:51 cri |
Borrell ya ce, kamar yadda ya sha nanatawa a lokutan baya, Amurka ta yi gaban kanta ta fice daga yarjejeniyar nukiliyar Iran a shekarar 2018, a don haka bata da ikon gabatar da shirin sake kakaba takunkumi kan Iran karkashin kudirin kwamitin sulhun MDD mai lamba 2231.
Domin tabbatar da yarjejeniyar hadin gwiwar ta JCPOA, Borrell yayi alkawarin cigaba da goyon bayan kiyayewa da kuma aiwatar da cikakkiyar yarjejeniyar ta JCPOA daga bangaren Iran da sauran bangarorin da batun ya shafa.
Ya bayyana yarjejeniyar a matsayin muhimmin ginshikin kawar da yaduwar makaman nukiliya a duniya, kana ya bukaci dukkan bangarori masu ruwa da tsaki dasu kiyaye yarjejeniyar kuma su guji daukar duk wani matakin da zai kara lalata yanayin da ake ciki a halin yanzu.(Ahmad)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China