Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kaso 60 na motocin bas dake sufuri a Sin sun koma amfani da makamashi mai tsafta
2020-10-26 09:52:43        cri

Yayin da kasuwar ababen hawa masu amfani da makamashi mai tsafta ke kara bunkasa a sassan duniya, ya zuwa 2020, Sin ta maye gurbin kaso 60 bisa dari na motocin bas dake sufurin fasinjoji a cikin kasar da samfuran masu amfani da makamashi mai tsafta, adadin da ya karu da kaso 20 bisa dari idan an kwatanta da na shekarar 2015.

Wasu alkaluma da hukumar lura da muhallin halittu da sauran sassan muhalli ta fitar sun nuna cewa, wannan nasara na da nasaba da aiwatar da matakan dake kunshe ne, cikin kundin sauye sauye dake cikin manufofin ci gaban kasa na shekaru 5 karo na 13, wanda kasar ta aiwatar tsakanin shekarun 2016 zuwa 2020, wanda ya tanaji bukatar samar da karin ababen hawa masu aiki da lantarki, don maye gurbin masu amfani da mai.

Ma'aikatar ta kara da cewa, domin biyan bukatun masu nasaba da wannan manufa, a farkon watan Oktobar nan, majalissar gudanarwar kasar Sin, ta amince da kara bunkasa masana'antun kera ababen hawa masu amfani da makamashin mai tsafta, manufar da za ta ingiza fasahohin da sashen ke bukata, da gina muhimman ababen bukata kamar wuraren caji, da karfafa hadin gwiwar kasa da kasa a fannin. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China