Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Makamashi mai tsafta jigon farfado da tattalin azrikin nahiyar Afrika
2020-07-11 17:03:05        cri
An bayyana kara inganta amfani da fasahohin raya makamshi mai tsafta, a matsayin jigo wajen gaggauta farfado da tattalin arzikin nahiyar Afrika, bayan mawuyacin halin da ya shiga sanadiyyar annobar COVID-19.

A cewar wani rahoto mai taken "makamashi mai tsafta a Afrika: wata dama a lokacin da ake fuskantar kalubale", karfin nahiyar na farfado da tattalin arziki bayan koma bayan da ya samu sanadiyyar annobar COVID-19 ya dogara ne da zuba jari kan hanyoyi masu tsafta na samar da lantarki.

A cewar Landry Ninteretse, shugaban kungiyar kiyaye muhalli ta 350Africa.org, daya daga cikin kungiyoyin da suka kaddamar da rahoton, makamashi mai tsafta ya dace kwarai da nahiyar Afrika.

Ya ce mutane da dama na rayuwa a wajen turakun lantarki na bai daya, a nahiyar dake da arzikin albarkatun iska da ruwa da rana, yana mai cewa, ya kamata a raya wadannan albarkatu domin biyan bukatun dukkan jama'a.

Rahoton wanda wasu kungiyoyi masu yaki da sauyin yanayi suka kaddamar, ya kuma bayyana cewa, nahiyar na kan hanyar komawa amfani da makamashi mai tsafta kafin ta fuskanci koma bayan dake da alaka da COVID-19. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China