Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin Sin: Kungiyar kasashe masu magana da Faransanci ta kasa da kasa za ta taimakawa ayyukan MDD
2020-09-09 10:24:33        cri

Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya bayyana cewa, karkafa mu'amala tsakanin kwamitin sulhu na MDD, da kungiyar kasashe masu magana da harshen Faransanci ta kasa da kasa (OIF), zai kara karfafa hadin gwiwar bangarori daban-daban, da kiyaye zaman lafiya a duniya da yayata bunkasuwa na bai daya.

A jawabinsa ga MDD, wakilin na kasar Sin, ya bayyana cewa, kasar Sin tana maraba da kungiyar wajen ganin ta kara shiga ayyukan shiga tsakani, da bunkasa tattaunawa, da mutunta juna da warware bambance cikin lumana. Kasar Sin tana fatan kungiyar ta OIF, za ta kara shiga ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD, da taimakawa wajen kara kwarewar ma'aikatan tabbatar da zaman lafiya, ciki har da samar da horo a fannin koyar da harshe da sauran taimako a fannin tsare-tsare.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China