Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin Sin: Farin cikin jama'a shi ne babban 'yancin bil-Adam
2020-09-18 19:24:51        cri

Hukumar kare hakkin bil-Adama ta MDD ta gudanar da taronta karo na 45, daga ranar 16 zuwa 17 ga watan Satumba, don tattauna batun da ya shafi 'yancin samun bunkasuwa. Baki dayan kasashe masu tasowa, sun yi kira ga kasashen duniya, da su hanzarta aiwatar da 'yancin samun ci gaba, sun kuma bukaci hukumar kare 'yancin bil-Adama, da ta kara gudanar da bincike game da 'yancin samun bunkasuwa.

Wakilin kasar Sin ya yi nuni da cewa, annobar COVID-19, ta yi mummunan tasiri ga ci gaban tattalin arziki da rayuwar jama'a, ta kuma shafi burin kasashe masu tasowa na 'yancin samun bunkasuwa. Ya ce, ya kamata kasashen duniya, su hanzarta aiwatar da ajandar Addis Ababa, kuma kasashe masu ci gaba, su cika alkawuran da suka yi na samar da taimako, ba tare da gindaya wasu sharudda na siyasa ba, kana su kare tsarin kasancewar bangarori daban-daban da na cinikayya tsakanin sassa.

Jami'in na kasar Sin ya kuma bayyana cewa, rayuwar jama'a cikin farin ciki, shi ne babban 'yancin bil-Adama. A don haka, kasar Sin tana kira ga dukkan kasashe, da su martaba ka'idojin MDD game da 'yancin samun bunkasuwa a matsayin jagora, da mayar da jama'a a gaban komai, da nacewa ga kirkire-kirkire, da tsarin yin komai a bayyane da samun bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba, da kokarin aiwatar da ajandar samun dawamammen ci gaba nan da shekarar 2030, da kuma yayata kokarin 'yancin samun ci gaba.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China