Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tijjani Muhd Bande: Sin muhimmiyar mambar MDD ce dake sauke nauyin dake wuyanta
2020-09-16 19:14:59        cri

Shugaban babban taron MDD karo na 74, Tijjani Muhammad Bande, ya bayyana cewa, MDD na da matukar muhimmanci fiye da lokutan baya. Bande ya bayyana haka ne yayin zantawa da manema labarai, yana mai cewa, idan aka kalli batun annobar COVID-19, muhimmiyar rawar MDD wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duniya, da bunkasa ci gaba da kare 'yancin bil-Adama, duk sun bayyana.

Da ya juya ga batun cikar MDD shekaru 75 da kafuwa kuwa, ya ce, wajibi ne MDDr ta kara kaimi wajen kara kulla alaka tsakanin jama'a, tare da mutunta dukkan kasashe.

Da yake tsokaci game da rawar da kasar Sin take takawa a harkokin MDD, Muhammad Bande, ya ce, kasar Sin muhimmiyar mambar kasa da kasa ce, ba wai saboda karfin tattalin arziki da kayayyakin da take samarwa ba, amma saboda kasancewarta zaunanniyar mambar kwamitin sulhun MDD, da muhimmiyar rawar da take takawa a fannin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duniya. Haka kuma kasar Sin, ya kara da cewa, "A ko da yaushe tana taimaka min da ma aikin babban taron MDD, kana mambar babban taron MDD ce dake sauke nauyin dake bisa wuyanta".(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China