Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta yi kira da a gaggauta kawo karshen tashin hankali a Nijeriya
2020-10-24 20:40:20        cri
Majalisar kula da tattalin arziki da zaman takewa da al'adu ta Tarayyar Afrika, ta yi kira da a gaggauta kawo karshen tashin hankalin da ake yi a wasu sassan Nijeriya, wanda ya samo asali daga zanga-zangar adawa da zaluncin 'yan sanda.

Wata sanarwa da ta shiga hannun Xinhua yau Asabar a Lagos, ta ce majalisar na kira ga dukkan bangarori a kasar, ciki har da gwamnati da masu zanga-zanga, su hau teburin sulhu domin warware matsalar cikin hanzari da lumana, da nufin kaucewa kara ta'azzara al'amura. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China