Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU: COVID-19 ta haifar da matsanancin halin tattalin arziki da zamantakewa ga kasashen Afirka
2020-10-15 11:36:00        cri

Shugaban hukumar zartaswar kungiyar tarayyar Afirka ta AU Moussa Faki Mahamat, ya ce cutar COVID-19 ta haifar da matsanancin halin tattalin arziki da zamantakewa ga kasashen Afirka, matakin da kuma ya haddasa koma baya, ga nasarorin da nahiyar ta cimma a shekarun baya bayan nan.

Mahamat ya bayyana hakan ne ga taro na 37, na majalissar zartaswar kungiyar da ya gudana ta kafar bidiyo, a ranekun 13 da 14 ga watan Oktobar nan. Jami'in ya kara da cewa, hasashen da ake yi game da fadawar nahiyar cikin mashassharar tattalin arziki, sakamakon yaduwar cutar ta COVID-19 a karon farko cikin sama da shekaru 20 bai zo da mamaki ba.

Mr. Mahamat ya ce, cutar COVID-19 ta haifar da matsin lamba ga tsarin kiwon lafiyar Afirka, wanda da ma can ke da rauni. Daga nan sai ya bayyana bukatar da ke akwai ga nahiyar Afirka, ta ci gaba da aiwatar da kwararan matakai na yaki da wannan annoba cikin hadin gwiwa da managarcin tsari. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China