Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta tabbatar da amincin dake tsakaninta da nahiyar Afrika a lokacin da ake fuskantar kalubale
2020-10-24 15:56:33        cri
Mataimakin shugaban hukumar kula da ayyukan Tarayyar Afrika, Kwesi Quartey, ya ce kasar Sin ta tabbatar da amincin dake tsakaninta da nahiyar ta hanyar goyon bayan al'ummarta a lokacin da suke fuskantar kalubale.

Kwesi Quartey ya bayyana haka ne a jiya, yayin bikin karbar gudunmuwar kayayyakin yaki da annobar COVID-19 da Sin ta turawa Tarayyar Afrika, wanda ya gudana a hedkwatar tarayyar dake Addis Ababa na Habasha.

Da yake jaddada cewa Sin ta kasance mai mara baya ga nahiyar Afrika da al'ummunta a lokacin da suke fuskantar kalubale, jami'in ya yabawa Sin bisa irin goyon baya da taimakon da take ba nahiyar a irin wannan lokaci.

Ya ce sun karbi adadi mai yawa na kayayyakin yaki da COVID-19 jiya da rana. Kuma daga alakarsu da Sin, sun fahimci abun da ake cewa, aminci shi ne kasancewa tare a lokacin da ake cikin matsala.

Da yake mika gudummuwar a gaban wasu jami'an diflomasiyya da jami'an tarayyar, Liu Yuxi, shugaban tawagar Sin a AU, ya ce tun bayan barkewar annobar, Sin da Afrika ke taimakawa juna. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China