Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Zhao Lijian: An fitar da rahoto game yanayin kwadago tsakanin al'ummun Xinjiang bisa sahihan shaidu
2020-10-23 20:50:37        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce akwai shaidu dake tabbatar da cewa, al'ummun kananan kabilun dake jihar Xinjiang, na gudanar da ayyukan kwadago bisa radin kansu, ba tare da wata tilastawa ba. Kuma tuni aka tattara alkaluman bincike game da sahihancin hakan.

Zhao wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da ya gudana yau Juma'a, ya ce bayanan da aka fitar game da harkokin kwadago a Xinjiang suna kunshe da gaskiyar lamari, an kuma samar da su ne bayan zurfafa bincike na adalci.

Jami'in ya yi fatan karin masu hangen nesa daga al'ummun kasa da kasa, za su rungumi gaskiya da dalilai na hakika, tare da yin watsi da karairayi.

A baya bayan nan ne dai cibiyar bunkasa bincike ta Xinjiang, ta tattara bayanai tare da fitar da rahoto, game da yadda al'ummun kananan kabilu dake zaune a Xinjiang ke gudanar da harkokin kwadago, bayan yin nazari da bincike mai zurfi. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China