Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ya kamata Amurka ta dakatar da zargi kan laifin da ita ce ke aikatawa
2020-10-21 21:43:51        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Zhao Lijian, ya bukaci Amurka ta daina zargin kasar Sin, da laifin da ita ce ke aikata shi. Jami'in wanda ya yi wannan kira yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, a yau Laraba ya ce a baya bayan nan hukumar tsaron Amurka ta (NSA), ta zargi Sin da kasancewa barazana ga bayanan tsaron ta.

Zhao Lijian ya ce ko sau nawa aka maimaita karya, ba za ta sauya matsaya ta koma gaskiya ba. Don haka lokaci ya yi da Amurka za ta dakatar da zargi kan laifin da ita ce ke aikatawa. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China