Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta ci gaba da bude kofa ga waje tare da samar da karin gudummawar bunkasa tattalin arzikin duniya
2020-10-20 20:03:30        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Zhao Lijian, ya ce Sin za ta ci gaba da bude kofarta ga kasashen waje, tare da samar da karin gudummawa ta bunkasa tattalin arzikin duniya baki daya.

Jami'in na wannan tsokaci ne, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, inda a yayin taron na yau Talata, ya ce Sin za ta ci gaba da samarwa kasashen duniya kasuwa, da damammaki na samar da ci gaba, za ta kuma tallafawa farfadowa, da bunkasar tattalin arzikin duniya.

Alkaluman da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta fitar a jiya Litinin, sun nuna cewa, Sin ta samu ci gaban tattalin arziki da kaso 0.7%, cikin watanni 9 na farkon shekarar bana. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China