Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta bukaci Amurka ta daina nunawa dalibai Sinawa wariya
2020-10-21 20:37:25        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Zhao Lijian, ya bukaci Amurka ta daina nunawa dalibai, da masu bincike Sinawa dake Amurka wariya. Jami'in ya ce Sin za ta ci gaba da daukar matakai da suka wajaba, don kare hakkokin halal na Sinawa.

Zhao Lijian, wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa a yau Laraba ya ce Amurka ta shafe tsawon lokaci, tana fakewa da wasu dokoki tana muzgunawa, da tsarewa, da yiwa dalibai Sinawa dake zaune a kasar tambayoyi masu nasaba da zargi.

Kaza lika jami'in ya ce dalibai Sinawa da dama, sun sha fuskantar muzgunawa a filayen jiragen saman Amurka yayin da suke shirin barin kasar, inda a wasu lokuta ake bincika, ko ma kwace musu wayoyin salula, ko kwamfuta ko sauran kayayyakin su. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China