Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masu zuba jari daga kasashen ketare na kyautata zato game da kasuwannin kasar Sin
2020-09-17 11:00:32        cri

Jaridar The Wall Street Journal ta Amurka, ta wallafa wani bayani a jiya Laraba, wanda ke cewa, tattalin arzikin kasar Sin ya farfado cikin sauri a watan Agusta da ya gabata, kuma yawan kudin sayarwa don daidaikun mutane ya karu bisa na makamancin lokaci na bara, kuma a karon farko aka samu karuwar adadin a bana, abin da ya nuna cewa, bangare daya kawai dake samun koma baya a tattalin arzikin kasar ya farfado.

Gidan talibiji na CNN na Amurka ya ba da labari a ran 15 ga wata cewa, cutar ta jefa tattalin arzikin duniya cikin mawuyancin hali na samun koma baya, a yayin da tattalin arzikin kasar Sin na farfadowa.

Kafar Nihon Keizai Shimbun ta kasar Japan ta ba da labarin cewa, shugabannin wasu manyan kamfanonin Amurka, sun halarci bikin baje kolin kayayyakin kimiyya da fasaha na zamani da Sin ta gudanar ta kafar bidiyo a birnin Chongqing a ran 15 ga wata. Lamarin da ya bayyyana muhimmancin kasuwannin kasar Sin, a yayin da Sin da Amurka ke takara da juna ta fannin kimiyya da fasaha.

Ban da wannan kuma, jaridar "Financial Times" ta Birtaniya, ta ba da labari a ran 16 ga wata cewa, yawan mutanen da cutar COVID-19 ta harba ya ragu matuka a kasar Sin, kuma matakan da gwamnatin ke dauka na tallafawa tattalin arziki a fannin manyan ababen more rayuwa, sun zama dalilin farfadowar tattalin arzikin kasar Sin. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China