Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta shiga shirin COVAX ne domin samar wa kasashe maso tasowa alluran rigakafin COVID-19
2020-10-21 21:25:33        cri

Yau Laraba 21 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a nan Beijing cewa, dalilin da ya sa kasar Sin ta tsai da kudurin shiga shirin COVAX, shi ne kara azama kan samun alluran rigakafin cutar COVID-19 bisa adalci, da samar wa kasashe maso tasowa alluran.

A ranar 19 ga wata, darakta janar na hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesusu ya ce, kasashe da yankuna 184 ne suka shiga shirin na COVAX, don haka karin kasashe za su samu alluran yadda ya kamata kuma bisa adalci. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China