Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta inganta Masana'antar harkokin zirga-zirgar sararin samaniya ta kasar
2020-10-20 11:14:48        cri
Kasar Sin za ta inganta raya masana'anatar harkokin zirga-zirgar sararin samaniya yayin shirin raya kasa na shekaru 5 karo na 14, wanda zai gudana tsakanin 2021 zuwa 2025.

Fu Zhimin, babban injinya na kamfanin kera na'urorin sararin samaniya na kasar Sin CASIC ne ya bayyana haka, yayin taron kasa da kasa kan bangaren karo na 6 da aka yi a birnin Wuhan.

Taron wanda ya samu halatar kwararru da shugabannin kamfanoni sama da 200 daga kasar Sin da wasu kasashe 9, ya tattaunawa kan nasarori da makomar masana'antar.

A cewar Fu Zhimin, raya masana'antar za ta ingiza cigaban bangarori kamar na tattalin arzikin zamani da samar da na'urori masu kwaikwayon tunanin dan Adam da wasu sabbin kayayyaki na zamani.

Cibiyar samar da roka ta sansanin kula da harkokin zirga-zirgar sararin samaniya dake Wuhan, na da karfin samar da na'urorin harba roka 20 a kowacce shekara. Haka zalika cibiyar samar da tauraron dan Adam dake cikin sansanin, na da karfin samar da taurari 100 zuwa 200 da nauyinsu ba zai gaza ton 1 ba zuwa karshen bana.

Babban injiniyan ya ce, kasar Sin zata inganta hada hannu da kasashen wajen da kara ware albarkatu da fasahohi da na'urorin sararin samaniya. Ya kara da cewa, kasar na da burin samar da karin hidimomi a bangaren ga sauran sassan duniya, musammam kasashen dake cikin shawarar Ziri daya da hanya daya.

Taron ya kuma zama muhimmin dandalin musayar ra'ayi da hadin gwiwa a bangaren. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China