Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Xi zai halarci taron cika shekaru 70 da shigar sojojin CPV yakin dakile farmakin dakarun Amurka kan jamhuriyar dimokaradiyyar Koriya
2020-10-21 20:40:54        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, zai halarci taron cika shekaru 70 da shigar sojojin sa kai na Sin ko CPV a takaice, yakin dakile farmakin dakarun Amurka kan jamhuriyar dimokaradiyyar Koriya, tare da taimakawa kasar.

Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin koli na JKS, kuma shugaban hukumar zartaswar rundunar sojin kasar Sin, zai gabatar da muhimmin jawabi yayin taron, wanda za a gudanar a babban dakin taruwar jama'a dake nan birnin Beijing, da karfe 10 na safiyar ranar Juma'a. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China