Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta ba da gudummawa wajen hanzarta ayyukan yaki da fatara na duniya
2020-10-19 19:36:56        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Sin Zhao Lijian, ya ce Sin ta ba da babbar gudummawa wajen hanzarta ayyukan yaki da fatara na duniya, ta kuma tallafawa ayyuka rage fatara a sassan duniya baki daya.

Jami'in ya kara da cewa, tuni kasar Sin ta fitar da al'ummarta da yawansu ya kai sama da miliyan 800 daga kangin talauci, kamar yanda bankin duniya ya tabbatar da hakan. Burin Sin shi ne tsame daukacin al'ummun yankunan karkara daga kangin talauci a wannan shekara, tana kuma fatan samar da ci gaba mai dorewa, mai nasaba da kudurorin yaki da talauci shekaru 10 gabanin lokacin da aka tsara tun da fari. Hakan ya kasance wani muhimmin tarihi da Sin ta kafa a fannin yaki da fatara, da ma nasarar samun ci gaba mai dorewa cikin lumana ga duniya baki daya.

Zhao Lijian ya kara da cewa, har kullum Sin na samar da tallafi ga ci gaban kasashe masu tasowa gwargwadon karfin ta. Sin ta gina cibiyoyin nune nunen fasahohin noma na zamani har 24 a sassan kasashen Afirka, aikin da sama da mazauna yankunan kimanin 500,000 suka ci gajiyar sa. A daya hannun kuma, wani rahoton bankin duniya ya nuna cewa, ana sa ran ayyukan da za a gudanar karkashin shawarar "ziri daya da hanya daya" da Sin ta gabatar, za su tsame mutane miliyan 7.6 daga kangin matsanancin talauci, da karin wasu miliyan 32 daga matsakaicin talauci. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China