Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping: A yi kokarin karfafa huldar dake tsakanin jama'a da sojoji
2020-10-21 20:02:16        cri

 

 

 

A jiya Talata, aka yi wani biki na karrama hukumomi da daidaikon mutane, wadanda suka samar da gudunmawa ga aikin yaukaka hulda tsakanin fararen hula da sojojin kasar Sin, inda shugaba Xi Jinping na kasar ya halarci bikin, tare da jinjinawa mutanen da suka samu yabo.

Shugaba Xi ya taba bayyana cewa, karfafa hulda a tsakanin fararen hula da sojoji yana da matukar muhimmanci. Ya ce, abubuwan da suke tabbatar da sakamakon yaki, ba lallai ne su zamo ingantattun makamai da yawan sojoji ba. Yadda ake tsara ayyukan yaki, da imani da jan-hali na sojojin, da yadda ake samun goyon baya da taimako daga jama'a, su kan zama dalili mafi muhimmanci da ya sa ake samun nasara a yaki. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China