Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ra'ayin Xi Jinping dangane da harkar raya yankunan musamman na tattalin arziki
2020-10-15 13:43:18        cri

 

A jiya Laraba, an yi bikin cika shekaru 40 da kafa yankin raya tattalin arziki na Shenzhen a kasar Sin, inda shugaba Xi Jinping na kasar ya yi wani muhimmin jawabi. Shugaban ya yaba wa mutanen da suka taimakawa gina wannan yanki, tare da gabatar da manufofin raya yankunan musamman na tattalin arziki a kasar Sin.

Shugaban ya ce, yadda aka raya Shenzhen daga wani karamin kauyen dake bakin teku, zuwa wani babban birnin da yawan al'ummarsa ya wuce miliyan 10, cikin wasu shekaru 40, ya zama wani abun al'ajabi a duniya.

Ban da haka, ya takaita fasahohin da aka samu wajen raya birnin, inda ya ce dole ne a tsaya kan tsarin siyasa na gurguzu nau'in kasar Sin, da dora cikakken muhimmanci kan tabbatar da moriyar jama'a.

Haka zalika, ya jaddada muhimmancin ci gaba da gudanar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, inda ya ce, za a dage wajen gudanar da wani sabon tunani na raya kasa, da zamanintar da fasahar kula da birane, da mai da moriyar jama'a a gaban komai. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China