Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin kasar Sin na nacewa manufar ci gaba ba tare da gurbata muhallin halittu ba
2020-09-25 21:13:09        cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Wang Wenbin, ya ce, gwamnatin kasar Sin na nacewa manufar ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, tana kuma sanya matsayin wayewar kai a fannin kare muhallin halittu, daidai da sauran muhimman sassa na ci gaban tattalin arziki, da zamantakewar al'umma da raya al'adu. Kaza lika tana daukar fannin kare halittu masu rai daban daban da matukar muhimmanci.

Wasu rahotanni sun nuna cewa, mujallar "Nature" ta Birtaniya ta wallafa a ranar Laraba cewa, ci gaba da bacewar halittu daban daban, da kara lalacewar muhallin halittu, na yin mummunan tasiri ga rayuwar bil Adama da makomar sa, don haka ya dace sauran sassan duniya su lura da kwarewar Sin a fannin kare nau'o'in halittu masu rai daban daban. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China