Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Wenbin: Kasashen Larabawa sun gamsu da farfadowar tattalin arzikin kasar Sin
2020-09-25 20:47:36        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce a ranar Talata, jami'an Sin da na kasashe mambobin kungiyar Larabawa, sun gudanar da taron karawa juna sani ta kafar bidiyo, game da kwarewar Sin a bangaren shawo kan kalubalen tattalin arziki da ya biyo bayan fama da kasar ta yi da cutar COVID-19.

Wan Wenbin ya ce, kasashen Larabawa sun bayyana kudurinsu na yin hadin gwiwa da kasar Sin, suna masu bayyana ci gaba, da farfadowar da tattalin arzikin kasar ta Sin ya yi, a matsayi matakin da ya karfafa masu gwiwa matuka.

Da yake fashin baki game da taron, Mr. Wang Wenbin ya ce kwararru daga Sin, sun yi cikakken bayani game da tsare-tsaren da kasar Sin ta yi a fannin kandagarki da magance bazuwar annobar, da ma bunkasa harkokin raya tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasar. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China