Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bude babban taron cinikayyar hatsi na Sin karo na uku a birnin Fuzhou
2020-10-19 14:24:16        cri
Yau Litinin, an bude babban taron cinikayyar hatsi na kasar Sin karo na uku a birnin Fuzhou na kasar Sin. Taken taron na wannan karo shi ne "Hada kayayyaki masu inganci, karfafa ayyukan samar da hatsi, zurfafa mu'amalar dake tsakanin bangarori daban daban, da kuma inganta cinikayyar hajoji".

Gaba daya, fadin dakunan baje-koli na wannan taro ya kai murabba'in mita dubu 75, inda kamfanoni sama da 2600 suka yi rajistar shiga wannan taro.

A yayin bikin bude taron, shugaban hukumar kula da hatsi da adana kayayyaki ta kasar Sin Zhang Wufeng, ya bayyana cewa, an kira wannan taro ne a lokaci na musamman da kasashen duniya suke maida hankali kan batun samar da isasshen hatsi, da kuma bisa halin da ake ciki, wajen karfafa ayyukan hana yaduwar cutar numfashi ta COVID-19, domin inganta bunkasuwar tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar al'umma.

Ya ce, lardin Fujian ya kasance muhimmin lardi dake kan hanyar siliki ta teku na karni 21, kuma, babban lardi ne da ake yin cinikayyar hatsi. Ya kamata a ci gaba da raya kasuwannin hatsi ta hanyar karfafa cinikayyar hatsi da yin musayar hajoji a kasuwannni. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China