Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin na nazarin dokar kare bayanan jama'a
2020-10-14 11:16:00        cri
Mahukunta kasar Sin, sun fara tattauanawa kan daftarin dokar kare bayanan da suka shafi wani mutum, da nufin kara kula da yadda ake karba da amfani da bayanan.

A cewar daftarin, zuwa watan Maris na bana, kasar Sin na da mutane miliyan 900 dake amfani da kafar intanet da sama da shafukan website miliyan 4 da manhajojin da suka zarce miliyan 3.

Daftarin ya yi bayanin cewa, kare bayanan mutum ya zama daya daga cikin muhimman batutuwa dake ciwa jama'a tuwo a kwarya.

Daftarin dokar na kuma duba yuwuwar tunkarar matsalolin lafiya na gaggawa ko kare rayuka da lafiyar mutane a matsayin daya daga cikin lokutan da aka halatta amfanin da bayanan da suka shafi mutum, sannan ya jadadda cewa, dole ne kuma a kare bayanan a karkashin irin wannan yanayi.

Kare wasu muhimman bayanai kamar, launin fata da kabila da addini da lafiya da bayanan kudi da halin da mutum ke ciki, na daga cikin batutuwan da daftarin dokar ya tabo. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China