Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwararrun Sin: An samu kwayoyin cutar COVID-19 a kan akwatin adana abincin da aka kiyaye su cikin kankara
2020-10-18 16:16:58        cri
Cibiyar hana yaduwar cututtuka ta kasar Sin ta sanar a jiya Asabar cewa, yayin da aka yi binciken dalilin da ya haifar da barkewar cutar COVID-19 a birnin Tsingdao na kasar a kwanakin baya, an gano kwayoyin cutar masu rai a kan wani akwatin adana wani kifin da aka kiyaye shi a cikin kankara. Hakan ya zama karo na farko a duniya, da kwararru suka samu gano kwayoyin cutar COVID-19 masu rai a kan wani akwatin adana abinci, wanda aka kiyaye shi cikin wani muhalli mai sanyi, gami da tabbatar da cewa yadda aka taba akwatin adana abincin mai dauke da kwayoyin cuta ka iya sanyawa a kamu da cutar.

A cewar kwararrun kasar Sin, yadda aka gano kwayoyin cutar a wannan karo, ya nuna wannan kwayar cuta ka iya zama a kan akwatin adana abinci cikin wani dogon lokaci, idan an kiyaye abincin a cikin wani muhalli mai sanyi sosai, don haka mai yiyuwa ne, kwayoyin cutar ka iya samun damar shiga wata kasa, ta hanyar zama a kan abincin da ake kiyaye su cikin kankara. Sa'an nan idan akwai wani muhallin da ya dace, kwayoyin cutar ka iya sanya mutum harbuwa da cutar, kana yawancin masu kamuwa da cutar ma'aikata ne dake kula da wadannan abincin.

Sai dai cibiyar hana yaduwar cututtuka ta kasar Sin ta ce, ba a fuskantar hadari sosai a fannin samun abincin da kwayoyin cutar COVID-19 suka gurbata su, saboda cutar ba wata cuta ba ce da ake iya kamuwa da ita ta hanyar cin abinci. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China