Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Adadin kamfanonin yanar gizo a gundumomin kasar Sin masu fama da fatara sun kai miliyan 3.05
2020-10-16 13:07:19        cri

 

Kakakin ma'aikatar kasuwancin kasar Sin Gao Feng, ya ce ya zuwa karshen watan Satumban bana, adadin kamfanonin yanar gizo, dake hada hadar cinikayya a gundumomin kasar Sin masu fama da fatara 832, sun kai miliyan 3.05.

Gao Feng ya ce alkaluman rubu'i uku na farkon shekarar nan sun nuna cewa, kamfanonin gundumomin 832 masu fama da talauci, sun cimma nasarar yin cinikayyar kudin Sin har yuan biliyan 206.88, wanda hakan ya nuna karuwar kaso 24.1 bisa dari, idan an kwatanta da adadin da suka samu a lokaci irin wannan a bara.

Kaza lika, a dai wannan lokaci, kudin da aka samu daga sayar da albarkatun gona ta yanar gizo ya kai yuan biliyan 26.42, karin da ya kai na kaso 48.1 sama da na makamancin lokaci a bara. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China