Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kudin shigar magidanta a kasar Sin daga watan Janairu zuwa Satumba ya karu zuwa kaso 3.9
2020-10-19 13:55:41        cri

Alkaluman da hukumar kididdigar kasar Sin ta fitar, sun nuna cewa kudin shigar kowa Basine a cikin watanni tara na farkon bana, ya kai Yuan 23,781, kimanin dala 3,549. Karuwar kaso 3.9 cikin 100 bisa makamancin lokaci na bara.

Hukumar ta ce, bayan an cire farashin kayayyaki, kudin shigar da kowa ne magidanci ya samu, ya karu da kaso 0.6 kan na shekarar da ta gabata, karuwa ta farko da aka samu a irin wannan lokaci a wannan shekara.

Wannan na nuna cewa, tattalin arzikin kasar Sin ya karu da kaso 4.9 cikin 100 daga watan Yuli zuwa watan Satumba na wannan shekara, idan aka kwatanta da makamancin lokaci na bara. Wannan shi ne ci gaba mafi sauri, kan kaso 3.2 da aka gani  daga watan Afrilu zuwa watan Yuni na wannan shekara.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China