Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasuwanci ta yanar gizo ya canja kasar Sin
2020-09-28 15:41:36        cri

Yawan kudin dake shafar kasuwanci ta yanar gizo a kasar Sin ya kai kashi 36.2% na GDPn kasar Sin. Ba kawai ana samun karuwar alkaluma a wannan fanni ba, har ma hakan ya kawo babban juyin juya hali mai zurfi.

A lokacin aiwatar da babban shiri na shekaru biyar-biyar na raya kasa na 13, biyan kudi ta hanyar salula, da sayar da kayayyaki ta gabatar da shirin bidiyo kai tsaye a kan Intanet da dai sauran kimiyya da fasahar Digital, sun samu bunkasuwa matuka, inda har suka canja zaman rayuwar jama'a a yau da kullum. Matakin da ya ingiza bunkasuwar tattalin arziki a cikin kasar Sin, da ma duk duniya baki daya.

Takardar bayani kan bunkasuwar kasuwanci ta yanar gizo na kasar Sin na shekarar 2020, wanda kwalejin nazarin sakwani da sadarwa na kasar Sin ta gabatar, ya nuna cewa, a shekarar 2019, yawan kudin dake shafar wannan kasuwanci ta yanar gizo ya kai kudin Sin RMB Yuan triliya 3.58, wanda ya kai kashi 36.2% na GDP.

Kasuwanci ta yanar gizo ba ma kawai wani tunani ba ne, har ma ya kusa yin nisa, ya shiga zaman rayuwar jama'a. Wen Ku, darektan sashin raya sakwanni da sadarwa na ma'aikatar kula da harkokin masana'antu da sadarwa ya ce, ya kamata kasuwanci ta yanar gizo ya ba da jagoranci ga bunkasuwar tattalin arizkin kasar Sin nan gaba, kuma kamata ya yi a kara karfin tsai da tsare-tsare, da kara karfin nazari, da ingiza hadin gwiwa tsakanin bangarori daban-daban, ta yadda bunkasuwar kasuwanci ta yanar gizo zai samar da sabbin damammaki ga bunkasuwar tattalin arzikin kasar, matakin da zai baiwa kasar Sin karfin takara a zamanin yanar gizo. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China