Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi: Hadin gwiwar Sin da Afirka ba za ta daina bunkasa ba
2020-10-16 20:07:33        cri

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya bayyana cewa, hadin gwiwar Sin da Afirka, ba za ta daina ci gaba ba, haka ma dandalin tattaunawar hadin gwiwar sassan biyu (FOCAC) ba zai daina bunkasa ba.

Wang Yi wanda ya bayyana haka Jumma'ar nan, cikin wani sharhi mai taken "Shekaru 20 na tafiyar bai daya ta cimma sabbin sakamako a sabon zamani" don murnar cika shekaru 20 da kafuwar dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka, ya kuma yi kira da a kara hada kai, albarkacin dandalin na FOCAC, da cimma manyan nasarori a tafiyar da ake ta gina makomar bai daya tsakanin al'ummomin Sin da Afirka.

A cewarsa, a cikin shekaru 20 da suka gabata, dandalin na FOCAC ya hade ginshikan siyasa na sassan biyu, da samun manyan sakamako a bayyane, da kara musaya tsakanin al'ummomin kasashen biyu, baya ga karfafa goyon bayan juna.

Ya ce, dandalin wata kafa ce ta kara bunkasa alakar Sin da Afirka, yayin da sassan biyu ke kokarin sadaukar da kai, da tuntuba, da hadin gwiwa da bunkasa alakar moriyar juna, da goyon bayan juna a lokacin wahala ko dadi da bude kofa da hadin kai.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China