2020-10-15 11:19:16 cri |
Ofishin MDD mai kula da ayyukan jin kai ko OCHA a takaice, ya ce karuwar adadin sojoji dake tattaruwa a yankin Sirte na kasar Libya, na haifar da damuwa, ta yiwuwar tsundumar al'ummun yankin kusan su 125,000 cikin yanayi na bukatar agajin jin kai.
Ofishin OCHA ya ce, abokan huldar sa na nuna damuwa, bisa halin dar dar da ake ciki a wannan yanki, sakamakon barazanar ayyukan soji.
A yanzu haka dai tallafin OCHA ya kai ga adadin 'yan kasar Libya masu samun mafaka a cikin kasar kimanin su 75,000, da rukunin masu rauni mutum 128,000, da sauran wadanda tashe tashen hankulan kasar suka shafa, da wadanda suke dawowa daga gudun hijira, da 'yan ci rani da 'yan gudun hijira 66,000, adadin dai ya kai biyu bisa uku na daukacin mutanen da ofishin ke fatan agazawa.
Kaza lika OCHA ya ce, bullar cutar COVID-19 a Libya ya kara dagula al'amura, inda ya zuwa ranar Talata, adadin wadanda suka harbu da cutar ya kai mutum 44,985, ciki har da mutum 656 da suka rasu sakamakon kamuwa da ita. (Saminu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China