Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugabannin Algeria da Tunisia sun zanta game da batun kasar Libya
2020-10-13 10:25:24        cri
Shugaban kasar Algeria Abdelmadjid Tebboune, da takwaransa na Tunisia Kais Saied, sun tattauna ta wayar tarho a jiya Litinin, don game da halin da ake ciki a kasar Libya.

Kamfanin dillancin labarai na APS ya ce, yayin zantawar tasu, shugaba Tebboune ya jaddada matsayin kasarsa, na goyon bayan matakan siyasa, na wanzar da zaman lafiya, wadanda ke da tushe daga al'ummar kasar. Mr. Tebboune ya kara da cewa, Algeria za ta yi duk mai yiwuwa, wajen taimakawa al'ummar kasar Libya, a yunkurinsu na zakulo hanyoyin wanzar da zaman lafiya ta hanyar gudanar da sahihan zabuka.

Kaza lika shugaban na Algeria, ya yaba da shawarwari da ake shirin gudanarwa tsakanin sassa daban daban na kasar Libya, cikin wata mai zuwa a birnin Tunis, karkashin lemar MDD. Shugabannin biyu sun kuma tattauna, game da ziyarar da shugaba Tebboune ke fatan gudanarwa a Tunisia, ko da yake ba su tsaida takamaiman lokacin ta ba. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China